Gwamnatin jihar Kaduna bisa jagorancin gwamna Dr. Nasir El-Rufa’i ta rushe wa mabiya ɗariƙar Shi’ah makaranta da abiti a Rigasa karamar hukumar Igabi Kaduna.
Zuwa yanzu ba wani kwakwkwaran dalilin da yasa aka rushe asibitin da makarantar.
Mabiyan na Shi’ah ƙarƙashin jagoran su na jihar Kaduna Umar wanda ake masa laƙabi da (Tirmizi) yace dokar ƙasa ta basu damar mallakar wurare a ko ina a ƙasar nan.
Sannan ya ƙara dacewa yanzu haka suna gaban kotu.

