Matatar Babban Dan Kasuwar Nan Na Duniya Aliko Dangote Zata Fara Aiki Yau Ɗinnan. 22/05/2023

Matatar Man Fetur mafi girma a yankin Afrika wacce zata dinga fitar da gangar ɗanyen man fetur dubu dari shida da hamsin (650,000), inda aikin ya lashe sama da dalar amurka 19.

Yayi tunanin yin matatar tin a shekarar 2013 inda a lokacin kuɗin aikin ya kama dalar amurka 9, a inda kamfanin sa ya bada kashi 1 cikin uku na kuɗin, sai aka ciyo bashin dala 6.

An so fara aikin matatar man fetur ɗin tun a shekarar 2016

Sakamakon chanjin wajen da za’a yi matatar zuwa lekki sai aka jinkirta aikin zuwa 2016, saboda kwazazzabu da sauransu.

Duba da wasu ayyukan da Dangote Group keyi, an so a buɗe wannan matata a shekarar 2018 amma ba’a samu damar hakan ba.

A watan July 2022 Dangote ya aro maƙudan kudade da adadin su yakai Biliyan 187 na Naira, kwatankwacin dalar amurka miliyan 442, kashi 12.7% zuwa 13.5% domin ganin aikin ya kammalu, ganin an ɗage bude matatar karo na 3 a shekara 4, sannan anan tsoron kamfanunuwan da aka karbo kudi a hannunsu, sannan sauran matatun gwamnati guda huɗu zasu yi gyare-gyare don ganin aikin su ya tafi yadda Yakamata a 2023.

A watan Janairu na 2023 aka fitar da sanarwar matatar zata fara aiki a ƙarshen wata ukun farko na wannan shekara da muke ciki.

By:

Posted in:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started