An ƙiyasata cewa mata sama da 50 ne ke ci gaba da zama a hannun masu ta da ƙayar baya na yankin renon Ingila da ake kira Ambazoniya bayan sun yi garkuwa da su a birnin Bamenda.
An kama matan ne bayan sun fito zanga-zangar lumana domin neman zaman lafiya a yankinsu bayan an kwashe shekaru suna rayuwa cikin tashin hankali da ‘yan aware suke haddasawa.
‘Yan tawayen sun zarge su da cewa suna aiki da masu tonon asiri.
Rikicin ‘yan tawaye a yankin renon Ingila na Kamaru ya raba fiye da mutum miliyan ɗaya da muhallansu tun daga 2017.
Mata 50 Suna Hannun Yan Tada Ƙayar Bayan Ƙasar Kamaru

By:
Posted in:
