Neman Taimakon Gaggawa

Wannan bawan Allah Abdurrabba Idris Yahaya mutumin kirki ne, Course Mate dinane tare mukai karatu a Jami’ar Bayero dake nan Kano, a halin yanzu yana fama da cutar cancer wadda taci karfin sa har takai idanun sa baya gani sai da daya, a madadin Abdulrabba ina neman masa taimako gun al’ummar Annabi.

Abdulrabba yana daga cikin best Graduating Student na set dinmu! Guru ne a Chemistry kuma mutum ne mai kokari da taimakon abokan karatun sa! Nakan tuna yanda ya taimakeni a wajen koyamin Chemistry courses har nai passing. Kwarewarsa wajen iya koyarda chemistry tasa duk dakikantar mutum idan ya koya ma saika fahimta. Ya taimaki ɗalibai da yawa, ciki har da ni.

Abin tausayi, ciwon yanzu ya yi tsanani har takai rashin kudin aikin da za’ai masa yasa sun koma gida da zama, cutar duk ta cinye abinda suke dashi, a halin yanzu suna buƙatar taimako don biyan kuɗin aikin da za’ai masa.

Ina roƙonku da ku taimakawa Abdulrabba domin a samu ai masa aiki. Kowacce gudumawa, komai kankantarta, za ta kawo gagarumin sauyi a rayuwarsa.

Idan kuna son ba da gudummawar ku, ga lambar account dinsa a kasa:

Account Number: 3142608608
Bank Name: First bank
Account Name: Abdurrabba Idris Yahaya
Phone No: 07066711067

Har ila yau, ina roƙonku da kuyi sharing wannan post din ga abokai, dangi, da yan uwa domin ceto Abdul.

Zaku iya tuntuba ta ko lambar sa dake sama idan kuna da wasu tambayoyi ko kuna son ƙarin bayani.

Nagode.

By:

Posted in:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started