Dalilin da ya sa Majalisar Dattawan Najeriya ta yi zaman gaggawa ranar Asabar

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya ce sun yi zaman gaggawa ne a yau Asabar da zimmar amincewa da ƙudirin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi da gwamnati ta gabatar musu.

“Wannan ba zama ne da muka saba yi ba,” in ji shi. “Abin da muke son yi shi ne amincewa da sabon ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi saboda tanadin dokar [ta yanzu] zai ƙare a ƙarshen watan Yuni.

“Abubuwan da ke cikin dokar su ne tituna da gadoji, waɗanda ambaliyar ruwa da aka yi a 2022 ta rusa. Idan ba mu yi sauri ba ruwa ya sake lalata su, abu ne mai wuya a iya ceto su.”

Ƙudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu da na uku, duka a zaman na yau. Sai dai Ahmad Lawan ya ce suna so su amince da shi tare da Majalisar Wakilai don a samu damar aiwatar da shi bayan wa’adin watan Yuni.

Kazalika, sanatocin sun amince da ƙudirin yi wa Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) kwaskwarima, wanda shi ma ya tsallake karatu na ɗaya da na biyu da na uku.

By:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started