Gwamnan Kano ya kori fitaccen malamin addinin Islama Saleh Pakistan, diyar Sheikh Jafar daga hukumar alhazai

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kori babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jiha Muhammad Abba Danbatta.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa da safiyar Talata.

Gwamna Yusuf ya kuma amince da nadin Alhaji Laminu Rabiu a matsayin sabon ES na hukumar alhazai ta jihar.

An kuma kori shugaban hukumar alhazai Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan. Alhaji Yusuf Lawan ya maye gurbinsa.

Wata fitacciyar ‘yar kwamitin da korar ta shafa ita ce ‘yar marigayi malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Jafar Mahmud Adam, Malama Nana Aisha.

Sabbin mambobin kwamitin sun hada da:  Sheikh Abbas Abubakar Daneji, Sheikh Shehi Shehi Maihula, Amb. Munir Lawan,  Sheikh Isma’il Mangu, Hajia Aishatu Munir Matawalle, da  Dr. Sani Ashir.

Sanarwar ta ce ana sa ran wadanda aka nada za su karbe harkokin hukumar nan take domin ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2023.

By:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started