Jami’an hukumar tsaro ta SSS a safiyar ranar Talata sun hana jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC shiga ofishinsu dake Ikoyi, Legas.
Har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, jami’an hukumar SSS sun hana daukacin jami’an EFCC da ke ofishin da ke titin Awolowo Road, Ikoyi shiga ginin, kamar yadda Reporters Focus Hausa ta samu.
Wani jami’in EFCC ya shaida wa wannan jarida cewa, “har ma sun sanya tankar sulke don su tsorata mu.
Majiyoyi daga hukumomin biyu sun ce ana ci gaba da gwabzawa tsakanin hukumomin biyu kan mallakar ginin.
Da Dumi-Duminta… Hukumar SSS ta hana jami’an EFCC shiga ofishin Legas

By:
