By ..Huzaifa Usman Umar.
Farashin Man Fetur (PMS) wanda aka fi sani da man fetur yanzu ya koma N537 kamar yadda rahotanni suka ce gwamnatin Najeriya ta cire tallafin mai.
Kamar yadda shafin jaridar The Leadership ya ruwaito, Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC Ltd) ya sanya farashin man fetur a Abuja, Legas, da Kano a kan N537, N488 da kuma N540 kan kowace lita.
Wannan ci gaban da ya zo kwanaki bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa tallafin man fetur ya kare, duk da haka, ya jefa sassan da ke cikin rudani na masana’antar man fetur ta Najeriya.
SABO: Danna “NAN” don shiga rukuninmu na WhatsApp da karɓar sabbin labarai kai tsaye akan WhatsApp ɗin ku!
Shugaban Hukumar, Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority, NMDPRA, Mista Farouk Ahmed, wanda hukumarsa ke kula da harkokin sassan, har yanzu bai mayar da martani ga ci gaban ba.
A halin da ake ciki, shugaban kasar ya shirya ganawa da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC kan cire tallafin man fetur. Za a yi taron ne da misalin karfe 2:00 na rana a yau Laraba, 31 ga Mayu, 2023.

