Shugaban ya kuma nada Goerge Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.
By… Huzaif Usman
Yuni 2, 2023
Shugaba Bola Tinubu ya nada kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar sa.
Shugaban ya kuma nada George Akume Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).
Mista Akume, tsohon gwamnan jihar Benue, shi ne tsohon ministan ayyuka na musamman a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hakazalika, Mista Tinubu, a wata sanarwa a ranar Juma’a mai dauke da sa hannun Abiodun Oladunjoye, daraktan yada labarai a fadar gwamnati, ya bayyana Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata a ofishin mataimakin shugaban kasa.
Da duminsa: Tinubu ya nada Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikata, Akume a matsayin SGF

By:
Posted in:
