Me ya sa ake kwan gaba kwan baya a batun tsagaita wuta a Sudan?

Daga Coletta Wanjohi

Har yanzu Sudan na ci gaba da fama da mummunan tashin hankali sakamakon rikicin da ke tsakanin manyan janar-janar din soji biyu masu gaba da juna, duk kuwa da kokarin ganin an samar da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Duk wasu yunkuri na ganin an kawo karshen zubar da jini a kasar na kara dusashewa la’akari da yadda dakarun sojin Sudan din ke kauracewa dut wata tattaunawa da dakarun soji ta RSF.

A ranar Laraba, rundunar sojin kasar ta ce ba za ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka da Saudiyya ke son a yi ba, saboda kungiyar RSF ba ta mutunta yarjejeniyar ba, batun da ita ma RSF din ta zargi sojin kasar da yi.

Wannan sabon al’amari dai ya dada sanya fargaba ga zaman lafiya da ake fatan gani a Sudan.

Yakin, na neman mulki a kasa ta uku mafi girma a nahiyar Afirka, ya fara ne a ranar 15 ga Afrilu inda ya yi sanadin kashe mutum sama da 800, tare da raba sama da mutum miliyan 1.4 daga matsuguninsu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Ma’aikatar lafiya ta Sudan ta ce baya ga daruruwan mutane da suka mutu, kimanin mutum 5,500 ne suka jikkata a fadin kasar kawo yanzu.

Rikicin da ya haifar da mummunan yaki tsakanin dakarun sojin biyu a Sudan, ya kawo cikas ga shirin kasar na komawa mulkin farar hula da ake sa ran yi a shekarar 2024.

Yiwuwar samar da zaman lafiya zai yi wuya

Shugabannin Sojin Sudan da na RSF sun rike manyan mukamai a majalisar mulkin kasar tun bayan hambarar da tsohon Shugaba Omar al-Bashir daga karagar mulki bayan wani bore da aka yi a shekarar 2019.

By:

Posted in:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started