Daga. Sunusi K/Na’isa.
Sarkin Dorin Kano Alhaji Uba Muhammad shi yayi kira a lokacin da yake ƙarɓar Shugabanin Ƙungiyar masu maganin gargajiya ta ƙasa reshan Ƙaramar hukumar Gwale (NANTMP) a fadarsa.
Ya ce ta kiyayewa da ƙa’idojin aikin da neman Ƙarin ilimi gami da sanya tausayi. Sarkin Dorin Kano Alhaji Uba Muhammad yace tausayawa Al’umma da neman karin ilimi kawai shine zai bunkasa tare da dorewar sana’ar.
Alhaji Uba Kofar Na’isa , yayi magana mai tsaho dangane da tarihin sana’ar ɗori da kuma yadda ta ke bunƙasa har ya zuwa wannan zamani. Haka kuma ya yi alkawarin bada duk taimakon da ya kamata ga Ƙungiyar.
Ya Kuma godewa masarautar Kano, karkashin jagoranci Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa tallafi da goyan baya da take bawa masu sana’ar gargajiya a jihar nan.
Da yake jawabi Shugaban Ƙungiyar masu maganin gargajiya ta ƙasa reshen ƙaramar hukumar Gwale, Dakta Adamu Yusuf Kakan, ya ce sun gabatar da kansu ga fadar Sarkin Dori domin su jaddada mubaya’a gare shi tare da karin samun hadin Kai don tallafawa al’umar jihar Kano da ma makwanta baki daya.
Ya godewa Sarki tare da alƙawarin samar da cibiyar da zata hada kan masu sana’ar gargajiya a Karamar hukumar ta Gwale domin ci gaba da taimakon jama’a.
Domin Tallata Hajojin Ku Da Sauran Tallace-Tallace, A tuntuɓe Mu Ta Wannan Lambar – 08028120702,08098821106

