YADDA DALIBAI ZA SU NEMI BASHIN GWAMNATIN TARAYYA NA YIN KARTU A NIGERIA

Daga. Ali Rabi’u Ali (Daddy)

A yau Litinin 12 ga watan Yuni, shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar baiwa dalibai rancen kudi. Dokar wacce ta baiwa dalibai damar karbar bashin da babu ruwa, tsohon shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Masana a fannin ilimi dai na ganin dokar ta baiwa jami’o’i yancin sanya kudin makarantar yadda suke so.

Tuni dai wasu jami’o’i suka fara kara kudin makarantun su.

A sabuwar dokar dai dalibai zasu iya neman bashin kudin ga shugaban bankin kula da ilimi ta hanyar makarantu bisa wadannan sharadan:



i. Dole ne dalibi ya samu gurbin karatu a daya daga cikin manyan makarantun Gwamnati; Abinda dalibi yake samu bai zarce dubu 500 a shekera ba; dole ne mai neman bashin ya gabatar da ma’aikatan gwamnati 2 da za su tsaya masa wadanda suka kai mataki na 12 zuwa sama ko kuma lauya wanda ya shafe shekaru 10 yana aiki.

ii. Dalibin da aka samu da kin biyan wani bashi a baya; ko wanda aka samu da laifin satar amsa yayin jarrabawa ko wanda aka samu da laifin shaye-shaye bazai amfana da bashin ba.

iii. Daliban da aka samu iyayensa sun gaza biyan wani bashi da suka ci a baya shima baza a bashi ba.

Biyo bayan aminta da wadannan sharadai, za a mika bukatar neman bashin ta hanyar ofishin jami’in dake kula da dalibai na kowacce makaranta inda za a fitar da jerin sunayen wadanda suka cancanta da samun bashin hade da wasikar amincewa daga shugaban makarantar da sashin kula da dalibai.

Dokar ta ce duk wanda ya amfana da samun bashin zai biya ne shekaru 2 bayan kammala hidimar kasa inda za a dinga daukar kaso 10 na albashinsa ko inda yake kasuwancinsa.

Ali Rabi’u Ali (Daddy)

Domin Tallata Hajojin Ku Da Sauran Tallace-Tallace, A tuntuɓe Mu Ta Wannan Lambar – 08028120702,08098821106

By:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started