Daga. Huzaif Usman
Wasu ‘yan ta’adda sun kashe manoma 25 tare da yin garkuwa da wasu mata da ‘yan mata daga al’ummomi daban-daban a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a ranar Juma’a a kauyuka biyar.
Wani shugaban al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan ta’addan sun zafafa kai hare-hare a kauyukan yankin a cikin makonni biyu da suka gabata.
Shima da yake tabbatar da harin, dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Neja ta Gabas, Mohammed Musa, ya koka da yadda ake samun karuwar hare-haren a kananan hukumomin Rafi, Paikoro, Munya da Shiroro.
Sai dai ya ce yana da kwarin gwiwar gwamnatin jiha da ta tarayya za su dauki nauyin lamarin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya ce an aike da ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji zuwa kauyukan Yakila, Tegina, Kagara, Pandogari, Kusherki da sauran kauyuka domin dawo da zaman lafiya a yankin.
Lamarin ya faru ne kwana guda bayan kashe ‘yan kungiyar ‘yan banga 13 tare da yin awon gaba da wasu mutanen kauyen a Kusharki.
Jihar Neja dai ta kasance cibiyar ‘yan ta’addan da aka fi sani da ‘yan fashi. Wannan kungiyar na ta’addancin kauyuka da matafiya suna saka haraji kan al’ummomin manoma da kuma sace mazauna garin domin neman kudin fansa.
Domin Tallata Hajojin Ku Da Sauran Tallace-Tallace, A tuntuɓe Mu Ta Wannan Lambar – 08028120702,08098821106

