A yayin wani biki na shekara-shekara da ake kira ‘Crepissage,’ dubban dubbai ne suka taruwa don gyarawa da kuma ƙarfafa tsarin da aka gina masallaci mafi girma a duniya wanda aka gina da ƙasa wato (Laka) kafin lokacin damina a watan Yuli da Agusta.

Maza da mata da yara kanana na dauke da banco – wato ƙasa chaƙude da, ruwa, shinkafa, man shea da garin baobab – wanda ke kare masallacin mai tsayin mita 20 daga zaizayar kasa sakamakon ruwan sama mai karfi da tsatsatsauran hali da yanayin zafi iya haifarwa.

An yi imanin cewa an fara gina masallacin ne a karni na 13, an gina masallacin ne ta hanyar amfani da kayan gida domin nuna irin gine-ginen yankin Sudano-Sahel na musamman. Taron sake gyarawa ba aikin kulawa ba ne kawai don tabbatar da wanzuwar masallacin, amma kuma ana yin shi ne a matsayin biki na girmama al’ummar Djenne, imani da al’adun gargajiya.
Tare da Timbuktu, birnin Djenne ya taka muhimmiyar rawa wajen fadada addinin musulunci a cikin nahiyar Afirka. Tun daga karni na 13, birnin ya zama wurin kasuwanci kamar yadda aka danganta shi da manyan hanyoyin kasuwanci da suka tashi daga gabar yammacin Afirka har zuwa gabar tekun Bahar Rum da Gabas ta Tsakiya.
A cikin sa’o’i na farkon ranar da ake sa ran, titunan birnin suna zuwa da rai tare da waƙoƙi da raye-rayen da aka yi a ƙarƙashin hasken wata – kuma da misalin karfe 4 na safe, buguwar busa ce ke nuna farkon bikin mafi mahimmanci na shekara.

