📸Huzaif Usman.
Rasmiyya Shamali ta haifi ‘ya’ya hudu – Najah, Abdel Rahim, Rakan da Rayan – bayan ta gaza yin amfani da maniyyin da aka yi fasa-kwaurinsa sau biyu a baya daga mijinta, Ahmed, wanda ke zaman gidan yari na shekaru 18 tun 2008.
Mahaifiyar Ahmed Najah ta ce ” Fursunonin na ci gaba da kalubalantar aikin ta kowane fanni, ciki har da ta hanyar fasakwaurin maniyi domin haifuwar jakadun ‘yanci,” in ji mahaifiyar Ahmed Najah.

Adadin yaran da iyayen suka haifa a gidan yarin Isra’ila cikin shekaru 10 da suka wuce ya karu zuwa 122 a bana, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.
An haifi yara maza uku da mace daya a asibitin Al Makassed da ke gabashin birnin Kudus a watan Mayu, kuma an aika da hotunansu ga mahaifinsu, wanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru uku.

