DA DUMI-DUMI: Jami’an DSS sun dakatar da shugaban EFCC, Bawa.

Huzaif Usman.

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da aka dakatar, Abdulrasheed Bawa, yana hannun jami’an tsaro na farin kaya (DSS).



An tattaro cewa Bawa ya isa hedikwatar DSS da misalin karfe 9:02 na dare.



Wata majiya ta shaida wa Politics Digest cewa a halin yanzu jami’an ‘yan sanda na sirri suna gana wa shugaban EFCC da aka dakatar.



Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar da kasancewar Bawa a hannun su, a wata sanarwa da ta samu daga Politics Digest.



Sai dai bai yi cikakken bayani kan abin da ‘yan sandan sirrin suka gayyaci Bawa ba.

By:

Posted in:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started