Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023, ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da damfarar yanar gizo a Legas.
EFCC ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis.
Wadanda ake zargin sun hada da Tamaraemi Akpoviri, Jonathan Oshioke Okhomode, Jordan O. Clifford, Okorie J. Christian da Enabule Peace Osaro, jami’an hukumar yaki da rashawa na shiyyar Legas ne suka kama su, a wani samame da suka kai a gidan Buena Vista Estate, Orchid. Road, unguwar Lekki dake jihar Legas, biyo bayan rahoton sirri.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin, a wurin da aka kama su, sun hada da manyan motoci, na’urorin hannu, da kwamfutocin tafi da gidanka.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun ba da kansu da kansu kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Credit: Twitter | Hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da damfarar Intanet a Legas

By:
Posted in:
