An Gamu da Gawar Ma’aurata Amurkawa A Otal din Mexico.

Ma’auratan Amurka, John Heathco, 41; da Abby Lutz, mai shekaru 22; An tsinci gawawwakinsu a cikin wani otal dinsu na alfarma na Hyatt na Mexico, a cikin fargabar cewa an ba su guba sakamakon ledar iskar gas a Baja California Sur, Mexico.

‘Yan sanda da ma’aikatan lafiya sun isa otal din Rancho Pescadero da misalin karfe 9 na daren ranar Talata, inda suka gano Amurkawa biyu maza da mata, bayan sun samu labarin cewa ma’auratan ba su hayyaci ba, kamar yadda Daily Mail ta ruwaito a ranar Alhamis.

‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutanen biyu a wurin wani katafaren otal da ke yankin tekun El Pescadero.

A cewar ofishin babban mai shigar da kara a ranar Laraba, ma’auratan sun mutu kusan sa’o’i 10 ko 11 a lokacin da aka same su kuma babu alamun tashin hankali a jikinsu.

A halin yanzu babban lauyan kasar yana sa ido kan binciken, biyo bayan bala’in da ya biyo bayan aukuwar irin wadannan mutane a kasar Mekziko sakamakon gubar da ake samu daga iskar carbon monoxide da ake samu ta hanyar iskar gas da kuma murhu da ba ta dace ba.

Daga Huzaif Usman

By:

Posted in:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started