Halin Da Wata Makaranta Ta Karamar Sakandiren Gwamnati A Sumaila Take Ciki.

KIRAN NEMAN AGAJI GA MAKARANTAR ƘARAMAR SAKANDIRE TA GARIN DAGORA DAKE ƘARAMAR HUKUMAR SUMAILA JIHAR KANO.

Daga Isah Adam Dagora

Waɗannan hotuna da kuke gani hotuna ne na wata ƙaramar makarantar Sakandire (Junior Secondary School) dake garin Dagora a ƙaramar hukumar Sumaila ta jihar Kano sakamakon iska da mamakon ruwan sama da aka samu ta yaye rufin ajujuwan ɗaukar darasi gaba ɗaya a ranar Talatar da ta gabata 14/6/2023.

Wannan makaranta tana ɗauke da aƙalla ɗalibai sama da Ɗari Biyu wanda suke zuwa neman ilimi daga garuruwa kamar haka duk a faɗin ƙaramar hukumar Sumaila; Garin Ɓeta, Madobi, Gudalai, Gajiki, Gidan Igai, Takwaɓe, Rum, Gangare, Kukar Lema da sauran su.

Muna kira ga masu madafun iko daga matakin Tarayya da Jiha harma da masu hannu da shuni da a duba halin da wannan makaranta take ciki da kuma yadda abin zai shafi karatun waɗannan ɗalibai mussaman la’akari da yanayin damina a kawo ɗauki da wuri.

By:

Posted in:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started