An tayarwa mazauna unguwar Salanta hankali da tsakar dare.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rusau a wani yankin cikin birnin kano.

Yanzu haka hankalin magidantan da iyalansu da yara ƙanana duk a tashe yake, inda magidantan suka fito dan kare haƙƙinsu.
Magidantan suna ganin cewa ba’a musu adalci ba a tashe su da tsakar dare. Inda yanzu haka sun kasa zaune sun kasa tsaye su da iyalansu.
Wata majiyar ma tace an saka musu duka daga su har iyalan nasu, wasu ma anyi musu jina-jina sannan harda mace mai ciki.

Shin yanzu ina zasu je a wannan
dare?


