A ranar Juma’a ne aka gano gawarwakin mutane hudu da suka hada da yaro dan shekara uku da wata yarinya ‘yar shekara 11 a wani gida da ke Landan.
A cewar Dailymail a ranar Asabar, an kira ‘yan sandan Metropolitan zuwa adireshin a Hounslow ranar Juma’a game da damuwa ga mazauna wani gida a Staines Road, Bedfont, a yammacin babban birnin Ingila.
An ce jami’an sun kutsa kai inda suka gano gawarwakin wani mutum da mace ‘yan shekaru 30 da haihuwa, wata yarinya ‘yar shekara 11 da kuma wani yaro dan shekara uku.
Ko da yake ana ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin sunan da kuma sanar da dangi na kusa, ‘yan sandan Birtaniyya sun bayyana cewa sun yi imanin sun san ko wanene mutanen hudu, wadanda ake kyautata zaton suna da alaka.
Babban Sufeto Sean Wilson, kwamandan ‘yan sanda na yankin yammacin London, ya ce, “Bincikenmu yana kan matakin farko, kuma bisa bincikenmu na farko, a halin yanzu ba mu neman kowa dangane da lamarin.
“Na san kadu da damuwa da wannan mummunan al’amari zai haifar a tsakanin al’ummar Hounslow da kuma wajen.
“Zan iya tabbatar wa mutanen yankin cewa kwararrun jami’ai suna aiki don gano ainihin abin da ya faru kuma zan ba da ƙarin bayani da zarar na samu.”
—
Ku biyo mu domin samun labarai da bidiyoyi masu kauri
Yara Biyu, Namiji, Mace An tsinci Gawarsu A Wani Gida A Landan

By:
