Kamar yadda muka yi alkawari, mun bude aikace-aikacen neman gurbin karatu na Postgraduate ga ’yan asalin Jihar Kano da ke da digiri na farko.
Ana gayyatar aikace-aikacen daga ƙwararrun masu digiri don gudanar da karatun digiri na biyu a cikin Jami’o’in Najeriya da na Waje don tsarin inganta Ilimi na shekarar 2023/2024.
Kuna iya samun fom ɗin daga wannan link din 👇👇👇
http://www.kanostate.gov.ng/scholarship
Ina yiwa duk mai sha’awar fatan alheri. – AKY

