Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama wasu mutane hudu masu suna Hassan Adamu mai shekaru 18; Abdulaziz Abubakar, 20; da Abdullahi Shuaibu mai shekaru 25 da wani mutum guda bisa zargin satar awaki.
Da yake tabbatar da kamun su ga manema labarai, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mahid Abubakar, ya ce ‘yan kungiyar sun saba yin aiki da babur guda uku.
“Mutanen yankin Gombe sun yi aiki da rahoton sirri kan kungiyar barayin da suka kware wajen yin amfani da babura masu uku wajen satar awaki daga unguwar Malam Inna da Wuro Kesa, suna sayar da su. An kama su ne a maboyarsu daban-daban; wadanda ake zargin sun amsa da kan su cewa sun aikata wannan aika aika.”
Ya bayyana cewa mutane hudun da ake zargin sun amsa laifinsu.
“Har yanzu ana ci gaba da bincike kuma nan ba da dadewa ba za a kai karar zuwa kotu. Abubuwan da aka gano sun hada da babur mai uku da akuya daya.”
An kama wasu mutane hudu da laifin satar akuya a Gombe

By:
Posted in:
