Kare hakkin ‘yan jarida, Gwamna Otti ya fadawa shugaban NGE

Gwamnan Abia ya yi kira da a inganta aikin jarida a Najeriya.

By Reporters Focus Hausa



Yuni 22, 2023


Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya yi kira ga Eze Anaba, zababben shugaban kungiyar Editocin Najeriya (NGE) da ya yi kokarin kare ‘yancin ‘yan jarida da kuma inganta kwarewa.

Mista Otti ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Kazie Uko, kuma ya bayyanawa manema labarai a Umuahia, ranar Laraba.

Gwamnan ya bayyana cewa fitowar Mista Anaba a matsayin shugaban kungiyar wata babbar shaida ce ta halayensa na jagoranci da kuma nuna kwarin gwiwa da abokan aikin sa suka yi masa.

Ya bukaci Mista Anaba da ya yi amfani da sabon ofishin nasa wajen inganta jin dadin ‘yan jarida da kuma bunkasa sana’ar aikin jarida a kasar.

Gwamna Otti ya taya Mista Anaba murnar fitowar sa tare da yi masa addu’ar Allah ya ba shi nasara da zai ci gaba da karfafa hadin kai da ci gaban kungiyar.


Ya kuma taya daukacin kungiyar murna, sannan ya yabawa kwamitin shirya taron, bisa tabbatar da an gudanar da zabe cikin gaskiya da kwanciyar hankali wanda ya samar da sabbin shugabannin.

“Hakika al’ummar jihar Abia sun yi farin ciki da samun ku a matsayin daya daga cikin jiga-jigan ‘ya’yansu, kuma suna fatan za ku yi amfani da sabon ofishin ku don yin aiki don cimma burinsu na samun ci gaba da wadata a Abia,” in ji Mista Otti.

By:

Posted in:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started