Zan binciki shari’ar dala ta Ganduje – Shugaban yaki da cin hanci da rashawa na Kano.

Daga Huzaif Usman

Muhuyi Magaji, Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ya ce zai sake bude wani bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

Ku tuna cewa a watan Oktoban 2018 ne jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani faifan bidiyo na Ganduje da ake zargin yana karban makudan daloli tare da cusa baragurbin a cikin farar rigar sa ko kuma ‘babanriga’. An kuma yi zargin cewa ya nemi dala miliyan 5 daga hannun ‘yan kwangilar da suka nadi bidiyon.

Magaji wanda Gwamna Abba Yusuf ya mayar da shi, watanni bayan da Ganduje ya sauke shi daga mukaminsa bisa zarginsa da cin zarafinsa, ya shaida wa Aminiya cewa ba za su iya bude wani bincike a kan tsohon Gwamnan ba a lokacin da yake kan mulki saboda yana da kariya.

Yace;


“Lokacin da na ce zan binciki lamarin dalar Ganduje, shi ne gwamna mai ci… Ina aiki a karkashinsa. balle yanzu da ya zama tsohon gwamna?

“Don haka duk maganar da na fada nake nufi. A lokacin na ce muku za mu bude bincike kuma muna kan bincike.

“Amma akwai wasu iyakoki, domin duk wani gwamna mai ci, mataimakin gwamna, shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa yana da kariya a tsarin mulkin Najeriya.

“Don haka akwai iyaka ga abin da za mu iya yi. Yanzu, iyaka ba shi da ƙari. Hukumar za ta yi abin da ya dace.”

By:


Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started