Rundunar shiyyar Kaduna ta hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta samu hukuncin dauri kan wani shahararren mawakin TikTok, Crown Uzama, da wasu mutane biyar da suka hada da Bethel Makuochukwu, John Joseph, Favor Chidiogo Emmanuel, Abdul-Azeez Suleiman Temidayo, da Joel Kator.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin Twitter ranar Juma’a.
An same su da laifin karkatar da kudade. Dukkansu sun amsa laifin da ake tuhumarsu da su a gaban mai shari’a A. A. Isiaka.
A wani bangare sanarwar ta kara da cewa, “Mai shari’a Isiaka ya yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari tare da zabin biyan tara.
“Bugu da kari, za su yi awon gaba da duk wasu na’urorin lantarki, daki da sauran kayayyakin da aka kwato daga hannunsu, ga gwamnatin tarayyar Najeriya.
“An kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban a Kaduna bisa bayanan sirri da rundunar ta samu. Binciken da aka yi ya tabbatar da cewa sun yi kama da wasu ‘yan kasashen waje kuma sun yi amfani da bayanan karya wajen damfarar wadanda ba a san ko su wanene ba.”
Credit: Twitter | Hukumar EFCC
—
Ku biyo mu domin samun labarai da bidiyoyi masu kauri
Kotu Ta Daure Wani Ɗan TikTok, Da Wasu Biyar Don Zamba a Intanet

By:
Posted in:
