Mai Rahoto. Huzaif Usman

Hakan dai ya biyo bayan kashe wani matashi mai suna Yusuf mazaunin unguwar Sheshe da wasu ɓatagari suka yi a Kwanar Goda.
Lamarin da ya janyo samun rikicin tsakanin unguwannin sai dai ƴan sanda sun kawo ɗauki inda suka kora matasan da suka yi yunƙurin neman ɗaukar fansa
Yanzu haka dai tuni unguwannin suka ɗaɗe inda aka rufe shaguna da gidaje.
Dama an ɗauki tsawon lokaci ana zaman doya da manja tsakanin ɓatagarin matasan da ke waɗannan unguwanni.
Kawo lokacin haɗa wannan rahoto hukumomin tsaro ba su ce komai ba a kai.

