Babban Fasto na Cocin The Evening Church da ke Uyo, jihar Akwa Ibom, Runcie Mike, ya mutu kwanaki biyu bayan ya jagoranci jana’izar daya daga cikin mambobinsa, ‘yar shekara 36 ga wani shahararren mai yada labarai.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Fasto wanda cocinsa ke a shagon sayar da kayayyaki, Tropicana Centre, Uyo an ce ya rasu ne a ranar Asabar 1 ga watan Yuli a Uyo.
Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya biyu, an ce ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.
Lokacin da labarin ya fito, yawancin ƴan cocin sun ɗauka cewa labarin karya ne. Amma daga baya shugabancin cocin ya tabbatar da faruwar baƙin cikin.
“A wannan lokacin baƙin ciki, muna umurci jikin Kristi ya riƙe mu cikin addu’o’i kuma musamman, danginsa na kusa,” in ji shugabancin cocin.
Shahararren limamin cocin Akwa Ibom ya rasu kwanaki biyu bayan jagorantar wata jana’iza.

By:
Posted in:
