Daga. Huzaif Usman

A gaskiya Bayero Bayero University, Kano, NigeriaBayero University, Kano, Nigeria Bayero University, Kano, NigeriaBayero University, Kano, Nigeria Nigeria da malaman jami’a Abun naku yazo da zalunci da nuna halin ko in kula ga ƴaƴan talakawa. Kun sa kuɗin makaranta wanda ya gagari ƴayan talakawa biya, sannan cikin ɗaliban da suka biya kuɗin su kawo yanzu kashi 1 bisa 3 na ɗalibai basu biya wannan kuɗin ba. Ance ku taimaka kuyi tsarin part-payment kunce ba haka ba, wannan kora da hali kenan.

Makwabtanku a Katsina wato Federal University Dutsinma Katsina part-payment suke, meyasa ku ba zaku tausaya ba.
Ance to zakuyi applying entrepreneurship tin daga aji na farko har ajin ƙarshe, amma kunce baku da skills ɗin, sannan zaku yaye ɗalibai kamarku marasa skills wanda basu san inda zasu dosa ba. Saboda da son zuciya kuma kunce idan ana so ku koya wa ɗalibai entrepreneurship sai gwamnati tayi empowering ɗinku kun samo skills ɗin sannan zaku koya musu, sannan duk da haka kunce wai aiki ne zai muku yawa. Sannan fa ko sun yarda zasuyi hakan ba a wannan session ɗin zasu fara ba.
Ana cikin wannan tirka-tirka ƙudin faculty da ɗalibai zasu biya da sauransu kun saka maƙudan kuɗaɗe, musamman allied science da clinical student.

Yanzu student da yake a Allied science zai biya kuɗaɗe da ba zasu gaza 180000 ba, ahaka ma banda hostel da sauran gyare-gyare, sannan za’a bar ɗalibi da siyan handouts.
Wannan tabbaci ne na nuna halin ko in kula.
Haba a tausayawa talakawa mana.

